Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta Sin ta amince da ayyukan zuba jari na dala biliyan 194 a 2019
2020-01-19 16:44:33        cri

Hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta ce kasar ta amince da manyan ayyukan zuba jari kan kaddarorin kasa 157 wadanda suka tasamma RMB yuan tiriliyan 1.33 kwatankwacin dala biliyan 194.

Kaso mafi yawa na hannun jarin an zuba ne a fannonin ayyukan sufuri da makamashi, a cewar Meng Wei, kakakin hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar.

Sauran ayyukan da suka ja hankalin hukumar sun hada da fannin fasahar zamani da tsimin albarkatun ruwa.

Adadin kaddarorin kasar Sin ya bunkasa sannu a hankali a cikin shekarar 2019, inda jarin fannin masana'antun fasahar zamani ya kasance a sahun gaba wajen samun bunkasuwa, kamar yadda alkaluman da mahukunta suka gabatar a Juma'ar da ta gabata.

Baki daya adadin kaddarorin kasar Sin ya karu da kashi 5.4 bisa 100 idan an kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2018, in ji hukumar kididdiga ta kasa wato NBS, kana jarin da aka zuba kan masana'antun fasahar zamani ya karu da kashi 17.3 bisa 100.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China