Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin cikin gidan Jamus bai yarda a hana Huawei shiga kasuwar fasahar 5G a kasar ba
2020-01-19 15:45:03        cri

Kafar yada labarai ta kasar Jamus ta ba da labari a jiya Asaba cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus Horst Seehofer ya shedawa manema labarai cewa, bai yarda a hana kamfanin Huawei na kasar Sin shiga kasuwar fasahar 5G a kasar ba, a ganinsa, idan Huawei ya kasa shiga kasuwar, lokacin gina Intanet na 5G zai dauki har tsawon shekaru 5 zuwa 10.

Horst Seehofer ya nanata cewa, ra'ayinsa game da wannan batu ya yi daidai da wanda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta dauka.

Dangane da ko za a ba da izni ga Huawei ya shiga kasuwar 5G ta Jamus ko a'a ya janyo hankalin jama'ar kasar sosai. Wasu 'yan siyasa sun ba da shawarar hana Huawei shiga kasuwar bisa dalilai na tsaron Intanet karkashin matsin lambar Amurka, amma yawancin mutane ciki har da Angela Merkel na ganin cewa, bai kamata a yi watsi da Huawei ba tare da gudanar da bincike ba.

An ce, majalisar dokokin Jamus za ta yanke shawara game da ko za a yi watsi da Huawei ko a'a nan wasu kwanaki masu zuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China