Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Myanmar
2020-01-18 17:20:03        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a wajen jerin bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Myanmar da kuma bikin shekarar yawon shakatawa ta kasashen biyu a birnin Naypyidaw, fadar mulkin Myanmar, inda ya ce, ya zama dole a inganta zumuncin gargajiya da ci gaba da raya dangantakar kasashen biyu a sabon zamanin da ake ciki, abun dake da babbar ma'ana kana ya kafa sabuwar alkibla ga makomar huldar kasashen biyu.

Duniya na fuskantar wasu manyan sauye-sauyen da ba'a taba ganin irinsu ba a tarihi. A wani bangaren, kasa da kasa na kara dogaro da juna, a dayan bangaren kuma, ra'ayin nuna bangaranci da na bada kariya na kara kawo barazana ga duk duniya, kuma ana kara fuskantar matsalar rashin adalci da daidaito tsakanin dangantakar kasa da kasa. A game da haka, shugaba Xi ya yi muhimmin jawabin, inda ya ce, a sabon zamanin da ake ciki, wasu muhimman ka'idoji biyar kan zaman lafiya da juna, ba su taba wuce yayi ba, domin suna iya taka muhimmiyar rawar a-za-a-gani. A matsayinsu na kasashen da suka bullo da ka'idojin biyar, ya kamata Sin da Myanmar su ci gaba himmantuwa wajen aiwatar da su, da kara marawa juna baya a harkokin MDD da hadin-gwiwar kasashen gabashin nahiyar Asiya, domin tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba a duniya baki daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China