Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su maimaita irin nasarar da suka samu wajen kafa yankin ciniki cikin 'yanci, kan shirin kawar da makamai a nahiyar
2020-01-18 16:55:41        cri
Yayin da shugabannin kasashen Afrika za su gudanar da taro a wata mai zuwa karkashin Tarayyar Afrika, kan shirin kawar da makamai a fadin nahiyar, kwararru sun yi kira ga masu tsara manufofi na nahiyar, sun maimaita irin hadin kan da suka yi wajen cimma yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci, game da kawo karshen rikice-rikicen dake tarnaki ga burin nahiyar na samun ci gaba.

Cibiya mai zaman kanta, ta nazarin harkokin tsaro ta nahiyar wato ISS, ita ce ta yi kiran cikin wata mukala da ta wallafa a baya bayan nan, mai taken "har yanzu rikici ne babban kalubalen ci gaban Afrika a 2020" wadda ta jaddada muhimmancin shugabannin nahiyar su sake hadin kai kamar yadda suka yi wajen kafa yankin ciniki mara shinge, domin kawar da makamai a nahiyar.

A cewar cibiyar, kamata ya yi shekarar 2020, ta zama muhimmiyar alama ga Tarayyar Afrika wajen kaddamar da shirin kawar da makamai, wanda ke da nufin kawo karshen yakin basasa da rikicin al'ummomi da cin zarafin wani jinsi da kare aukuwar kisan kare dangi a nahiyar, a shekarar 2020.

Mukalar ta kara da cewa, la'akari da cewa babu wanda zai musunta wannan gagarumin buri, tarayyar Afrika da mambobinta na bukatar aiki tukuru domin cimma burin ya zuwa karshen bana, musamman a lokacin da ake ganin an dauki turbar da ta dace. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China