Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zambia ta kaddamar da wata dabara ta rage tamowa
2020-01-17 09:48:24        cri
Gwamnatin Zambia ta kaddamar wasu dabaru 2 dake da nufin rage tamowa da inganta samar abinci mai gina jiki a kasar.

Kaddmar da shirin samar da abinci da sinadaran gina jiki da shirin kiwon lafiyar al'umma, za su taka muhimmiyar rawa wajen saita alkiblar inganta kiwon lafiya da samar da abinci mai gina jiki a kasar.

Daraktan sashen kula da ayyukan kwararru na ma'aikatar lafiya ta kasar, Kennedy Malama, ya bayyana yayin kaddamar da shirye-shiryen cewa, gwamnati za ta bude sabon babi a fannin kiwon lafiya ta hanyar kaddamar da wadannan shirye-shiryen biyu.

Ya ce ana sa ran shirye-shiryen su samar da ingantacciyar hanyar da ake bukata a yayin da ake kokarin magance muhimman batutuwan da suka shafi abinci mai gina jiki.

Daraktan ya kara da cewa, zuba jari a bangaren kiwon lafiya da samar da abinci mai gina jiki na da muhimmanci wajen tabbatar da bada damar samun kiwon lafiya na bai daya ga kowa a kasar.

A nata bangaren, wakiliyar asusun UNICEF a Zambia, Naola Skinner, yabawa gwamnatin kasar ta yi bisa kudurinta na inganta samar da abinci mai gina jiki bisa bullo da mabanbantan dabaru. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China