Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin kasar Sin na kara samar da kuzari ga tattalin arzikin duniya
2020-01-16 21:36:41        cri

 

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya fitar da sharhi mai taken "Shirin kasar Sin na kara samar da kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya" a yau Alhamis.

Sharhin ya dora muhimmanci kan taron shekara-shekara, na dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin duniya a shekara ta 2020, wanda za a shirya a mako mai zuwa, wanda takensa shi ne "Hada karfin kasa da kasa don cimma burin samun dauwamamman ci gaba", inda aka gabatar da batu, game da yaya za a inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya, a yayin da ake kara fuskantar rashin tabbas a fannin.

 

Sharhin ya ce, a cikin shekaru uku da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da amsa a taron Davos, wato "dunkulewar tattalin arzikin duniya ", hakikanin bukatu ne da ake kan ci gaban karfin samar da kayayyaki, kuma sakamakon dole ne na ci gaban kimiyya da fasaha."

Sharhin ya kara da cewa, a daidai bisa wannan manufar, a cikin wadannan shekaru uku da suka wuce, a yayin da ake fuskantar farfadowar ra'ayin bangaranci da ba da kariyar cinikayya, kasar Sin na iya tsayawa kan bude kofarta, da more dama da moriyar da ta samu, don tabbatar da cimma moriya da samun nasara tare.

 

Baya ga haka, sharhin ya ce, ana ta kara bukatar yin kwaskwarima kan tsarin gudanar da harkokin tattalin arzikin duniya. Ra'ayin da kasar Sin ta gabatar na tattaunawa tare kan manyan manufofin hadin kai, da kafa dandamalin hadin kai, tare kuma da more nasarorin da aka cimma kan hadin kai, ya kasance dabara mai amfani wajen gudanar da harkokin duniya.

Kasar Sin za ta ci gaba da inganta shawarar "Ziri daya da hanya daya", da inganta hadin kai a tsakanin bankin zuba jari na Asiya da bankunan na bangarori da dama, hakan ya kuma kara samar da kayayyakin amfanin jama'a masu inganci ga kasashen duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China