Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasan kwaikwayon gargajiyar Sinawa ya shiga wasu sassan Afirka
2020-01-16 20:48:56        cri
Nau'in wasan kwaikwayon gargajiyar Sinawa da ake wa lakabi da "Wuju" ya shiga wasu sassan nahiyar Afirka. Mashirya wasan sun bayyana cewa, yanzu haka sun kaddamar da nuna nau'in wasan a kasashen Najeriya, da Djibouti da kuma Tanzania, a wani mataki na bunkasa musayar al'adu tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A cewar Wang Xiaoping, shugaban tawagar nuna wasan daga lardin Zhejiang na kasar Sin, tun daga shekarar 2009, tawagar sa, ta gudanar da wasanni sama da 300, ga mutanen da yawan su ya kai miliyan 4.5 a kasashe da yankuna 46.

Wasan "Wuju" mai asalin lardin Zhejiang daga gabashin kasar Sin, na kunshe da kade kade dake da karin sauti 6 masu kayatarwa. Yana kuma da tarihi na sama da shekaru 500. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China