Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Sauyin siyasa ba zai yi tasiri ga dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ba
2020-01-16 20:05:49        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, sauyin yanayin siyasa ba zai yi tasiri ga dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ba. Ya ce ba wani sauyi da za a samu bisa dangantakar abokantaka irin ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni dake tsakanin kasashen Sin da Rasha, sakamakon sauyawar yanayin duniya, ko sauyin siyasa da ake fuskanta a kasashen biyu.

Kakakin ya bayyana haka ne a yau Alhamis, a yayin taron manema labaru, inda ya kara da cewa, murabus din firaministan kasar Rasha, da gwamnatin kasar, harkar cikin gidan Rasha ce, kuma a matsayinta na makwabciyarta kasar Sin, Sin din na girmama wannan sauyi.

A ranar 15 ga wata bisa agogon wurin, ba zato ba tsamani, firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ya sanar da murabus din gwamnatin kasar. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China