Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar Sin da Amurka dake kawowa juna moriya za ta amfani duk duniya
2020-01-16 02:15:35        cri

A ranar Laraba, mataimakin firaministan kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar Sin dake gudanar da shawarwari tare da kasar Amurka kan harkokin tattalin arziki, Liu He, da shugaban Amurka Donald Trump sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tattalin arziki da kasuwanci a tsakanin kasashen biyu a mataki na farko a birnin Washington, al'amarin da ya shaida cewa, an samu babban ci gaba ta fuskar daidaita takaddamar cinikayyarsu baki daya bisa muhimman shawarwarin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, wadanda aka shafe tsawon watanni 23 ana yinsu har na zagaye 13. Yarjejeniyar da aka daddale na dacewa da babbar moriyar Sin da Amurka da ma duk duniya baki daya, wadda za ta taimaka sosai ga tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a duniya.

Yarjejeniya a matakin farko ta kunshi ayoyi tara, wadanda suka jibanci hakkin mallakar fasaha, da musanyar fasahohi, da abinci da amfanin gona, da hidimomin hada-hadar kudi, da musanyar kudade, da fadada kasuwanci, da gudanar da bincike daga bangarori biyu gami da daidaita takaddama. Har wa yau, yarjejeniyar ta bayyana wasu muhimman batutuwa uku da kasar Sin ke tsayawa a kai, wato ya kamata a soke dukkan harajin kwastam da aka kara sanyawa hajojin kasar Sin, kuma ya kamata alkaluman kasuwanci su dace da hakikanin halin da ake ciki, har ma da inganta adalcin yarjejeniyar, tare kuma da wasu muhimman ka'idoji biyu, wato ka'idar WTO gami da ka'idar kasuwanni. Bugu da kari kuma, yarjejeniyar ta amshi bukatun da Amurka ke da su.

Cimma yarjejeniya a mataki na farko tsakanin Sin da Amurka ya nuna cewa, bangarorin biyu suna iya daidaita sabanin tattalin arziki da kasuwanci tsakaninsu ta hanyar gudanar da shawarwari cikin daidaito, abun da ya karfafa gwiwar a daidaita sabanin baki daya a karshe. Tarihi gami da hakikanan abubuwan da suke wakana yanzu sun tabbatar da cewa, idan Sin da Amurka sun yi hadin-gwiwa tare da zauna lafiya da juna, dukkansu za su ci moriya, amma idan sun yi fada da juna, kowane bangare zai sha wahala, al'amarin dai da ya kamata a lura lokacin da suke kokarin daidaita sabani da takaddama tsakaninsu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China