Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudin cinikayyar shige da ficen kasar Sin a shekarar 2019 ya kai sama da Yuan triliyan 31
2020-01-15 14:51:36        cri

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da kididdiga a jiya Talata cewa, yawan kudin cinikayyar shige da ficen kasar a shekarar 2019 ya kai kudin Sin RMB yuan triliyan 31.54, wanda ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa na shekarar 2018. Matakin da ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da rike matsayin kasa mafi karfi a duniya ta fuskar cinikayyar kayayyaki.

Masu sayayya na kasar Sin suna iya sayan abubuwan da aka shigo da su daga kasashen ketare cikin sawaba, ciki hadda amfanin teku daga Austriliya, barasa ta nahiyar kudancin Amurka, da kuma kayayyaki masu daraja daga Turai da sauransu. Yawan kayayyakin da Sin ta shigo da su daga ketare ya karu da kashi 19 cikin dari a bara, daga cikinsu kuma, ya'yan itatuwa, kayayyakin kwalliya, amfanin teku da aka shigo da su daga ketare ya karu da kimanin kashi 40 cikin dari.

Masarufin yau da kullum da Sin ta shigo da su daga ketare sun karu cikin sauri, matakin da ya ba da tabbaci ga ingancin bunkasuwar cinikayyar waje a bara. Alkaluma na nuna cewa, yawan kudin da Sin ta samu a fannin fitar da kayayyakinta zuwa ketare ya kai yuan triliyan 17.23 a bara, wanda ya karu da kashi 5 cikin dari, yayin da jimillar ta kai yuan triliyan 14.31 wajen shigo da kayayyaki daga ketare, wanda ya karu da kashi 1.61 cikin dari. Rarar kudin da kasar ta samu ta kai yuan triliyan 2.92, wadda ta habaka da kashi 25.4 cikin dari. Yawan kayayyakin shige da fice ya karu a ko wane watanni hudu. Abin lura shi ne, alkaluman cinikayyar shige da fice na watan Disamba sun kai wani sabon matsayi a tarihi, sun fi zaton mutane. Mataimakin shugaban babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Zou Zhiwu ya yi bayyani a gun taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya jiya, ya ce:

"Muna ganin cewa, Sin za ta ci gaba da rike matsayinta na farko a duniya ta fuskar cinikayyar kayayyaki a shekarar 2019. Kididdigar da WTO ta fitar a watan Janairu zuwa Oktoba na bara, ta nuna cewa, kasar Sin ta fi samun bunkasuwa a kasashe 10 dake kan gaba wajen fitar da kayayyakinsu zuwa ketare."

Ban da wannan kuma, a shekarar 2019, matsayin abokan cinikin Sin sun canja. EU ta ci gaba da zama abokiyar cinikayya mafi girma ta kasar Sin, yayin da kasashen kungiyar ASEAN suka zama na biyu. A cikin wannan shekara dai, yawan kudin cinikayyar shige da fice tsakanin Sin da ASEAN ya kai yuan triliyan 4.43, wanda ya karu da kashi 14.1 cikin dari, yayin da adadin Amurka a wannan fanni, ya kai yuan triliyan 3.73, wanda ya ragu da kashi 10.7 cikin dari, Japan tana matsayi na hudu, adadin da ya kai yuan triliyan 2.17, wanda ya karu da kashi 0.4 cikin dari. Dadin dadawa, kudin dake shafar cinikayyar shige da fice tsakanin Sin da kasashen dake cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya" ya kai yuan triliyan 9.27, wanda ya karu da kashi 10.8 cikin dari.

Ban da wannan kuma, kamfanoni masu zaman kansu sun maye gurbin kamfanoni masu jarin waje, suna kan matsayin koli ta fuskar cinikayyar waje a kasar Sin a bara. Yawan kudin cinikayyar waje na kamfanoni masu zaman kansu ya kai yuan triliyan 13.48, wanda ya karu da kashi 11.4 cikin dari, ya maye dukkan adadin a wannan fanni da fiye da kashi 40 cikin dari, matakin da ya ba da taimako wajen samun bunkasuwar cinikayyar waje da kashi 4.5 cikin dari. Zou Zhiwu ya ce:

"A bara, kamfanoni masu zaman kansu sun kara fitar da kayayyaki zuwa muhimman kasuwanni, kuma sun kara fitar da kayayyaki zuwa ASEAN, Latin Amurka da Afrika, wanda ya karu da kashi 25.6 da 11.4 da kuma 15.6 cikin dari bi da bi, saurin karuwar ta fi na karuwar da sauran yankunan kasar Sin suka samu a wannan fanni."

An ce, an samu kyautatuwar tsare-tsaren cinikayyar waje a bara, Zou Zhiwu ya ce:

"Sabuwar kididdigar da WTO ta fitar ta nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Satumba na bara, yawan kasuwa da kayayyakin injuna da latirori da kayayyakin dake bukatar ma'aikata da ayyuka da dama da suka mamaye a duniya, ya karu da kashi 0.2 cikin dari da kashi 0.9 cikin dari. Ban da wannan kuma, kayayyaki masu daraja da Sin ta fitar da su zuwa ketare sun samu karuwa yadda ya kamata, haka kuma, ana samun ci gaba sosai ta fuskar tallata tambura kirar kasar Sin, darajar kayayyakin da kamfanoni masu zaman kansu masu tamburan kansu suka fitar, ya kai yuan triliyan 2.9, wanda ya karu da kashi 12 cikin dari, wanda ya mamaye kashi 17 cikin dari na dukkanin kayayyakin da Sin ta fitar zuwa ketare, adadin da ya karu da kashi 1.1 cikin dari bisa na shekarar 2018."

Zou Zhiwu ya kara da cewa, ana zurfafa gyaran fuska da ake yi kan tsarin tattalin arzikin kasar Sin, ana tafiyar da manufofi da tsare-tsare yadda ya kamata, yanayin kasuwanci na rika samun kyautatuwa, kuma kamfanoni da kungiyoyi dake kasuwanni na kara nuna kuzari sosai, sannan an kyautata tsarin cinikayyar waje yadda ya kamata, ta haka za a taimaka wajen kara samar da makoma mai haske a fannin cinikin waje a shekarar 2020, kana za a samu bunkasuwar tattalin arziki mai inganci ba tare da tangarda ba a kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China