Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Turkiya ya bukaci dakarun alummar kasar Libya su tsagaita bude wuta
2020-01-15 10:51:44        cri

A jiya ne, shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan ya bukaci dakarun al'ummar kasar Libya su tsagaita bude wuta. Gwamnatin kasar Jamus ta bayar da sanarwa a wannan rana, inda ta ce za a gudanar da taron kasa da kasa kan batun kasar Libya a ranar 19 ga wannan wata a birnin Berlin na kasar.

Shugaba Erdoğan ya bayyana a gun taron majalisar dokokin kasar a jiya cewa, idan dakarun al'ummar kasar Libya sun ci gaba da kai hare-hare birnin Tripoli da sojojin gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar Libya dake birnin, kasar Turkiya za ta dauki matakai kan dakarun sojojin wanda Khalifa Haftar ke jagoranta.

Bisa sanarwar da gwamnatin kasar Jamus ta bayar a jiya, za a gudanar da taron kasa da kasa kan batun kasar Libya a ranar 19 ga wannan wata a birnin Berlin dake kasar, inda wakilai daga kasashe 11 ciki har da Rasha da Turkiya da sauransu, da hukumomin kasa da kasa ciki har da MDD, da EU, da AU, da AL da sauransu za su tattauna kan yadda za a warware rikicin kasar Libya cikin lumana. Firaministan gwamnatin hadin gwiwar al'ummar ta kasar Libya Faizi Sarraj da shugaban dakarun al'ummar kasar Libya Haftar za su halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China