2020-01-15 09:21:16 cri |
Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (ECA) ta jaddada muhimmancin bunkasa fasahar kirkire-kirkire a bangaren harkokin kudi, ta yadda hakan zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin nahiyar Afirka baki daya.
Hukumar ta bayyana haka ne jiya Talata, a daidai gabar da ta ke kira da a kara mayar da hankali a fannin kirkire-kirkiren harkokin kudi. Ta kuma ce, rahotonta na baya-bayan nan da za ta fitar kan tattalin arzikin Afirka a shekarar 2020 (ERA-2020), zai duba rawar da kirkire-kirkire a fannin harkokin kudi da fasahar kere-kere za su taka, wajen farfado da sashen kasuwancin Afirka.
Sauran fannonin da rahoton ECAn na watan Maris na wannan shekara zai duba, sun hada da matsayin kirkire-kirkire a fannin harkokin kudi a Afirka, da rawar da sassan biyu ke takawa wajen farfado da sashen kasuwancin nahiyar.
Haka kuma ECAn ta jaddada bukatar bayyana yadda za a ci gajiyar hanyoyin kirkire-kirkiren harkokin kudi, don bunkasa sashen kasuwancin nahiyar ta Afirka, bisa la'akari da tasirin kirkire-kirkiren a sashen hidimomin kudi da bangaren kasuwanci, wadanda suka hada da sabbin kamfanoni, kananan kasuwanci, kamfanoni masu hannayen jari da takardun lamuni, da kamfanoni gwamnati da masu zaman kansu. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China