Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikin waje na kasar Sin ya taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin duniya
2020-01-14 20:05:37        cri

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta bullo da sabbin alkaluman yau Talata, inda aka nuna cewa, a shekara ta 2019, jimillar kudin cinikayyar waje ta kasar ta kai Yuan triliyan 31.54, wadda ta karu da kaso 3.4 bisa dari, kuma jimillar kudin cinikin shige da fice ta kai matsayin koli a tarihi. A yayin da kasuwancin duniya ke tafiyar hawainiya, cinikin wajen Sin ya samu sakamako mai kyau, al'amarin da ya shaida irin dorewa da karfin da tattalin arzikin kasar Sin ke da shi, wanda ke taka muhimmiyar rawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

A halin yanzu, matsalar tawayar tattalin arziki, da karuwar dalilan rashin tabbas na kara damun dukkanin duniya, har ma cinikin wajen kasar Sin na ci gaba da fuskantar yanayi mai sarkakiya. Amma duk da haka, tsarin cinikin wajen kasar na kara samun ingantuwa. Kuma akwai yakinin cewa, yayin da cinikin waje na kasar Sin ke samun bunkasuwa yadda ya kamata, zai rika taka muhimmiyar rawa a fannin habaka tattalin arzikin dukkanin duniya baki daya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China