Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masallaci daya tilo da rundunar jajayen sojoji ta Red Army ta kafa a kasar Sin
2020-01-16 15:29:42        cri

 

 

 

 

Masallacin Hong Guang ke nan, masallaci daya tilo da rundunar jajayen sojoji ta Red Army a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kafa a kasar. A shekarar 1937, wasu mayakan rundunar jajayen sojoji sojoji suka sha kashi a yakin da suka gwabza da madugan mayakan sa kai dubu 100 sakamakon karancin mutane. A yayin da suke aikin karfi a kauyen Hong Guang wato gundumar Xunhua ta kabilar Salar, sun yi kokarin gina wani masallaci don girmama addinin musulunci da mazauna wurin suke bi. Fadin masallacin Hong Guang, ya kai kusan muraba'in mita 2700. A shekarar 2006, kasar Sin ta mai da masallacin a matsayin wurin al'adu da kasar ta dora muhimmanci don kiyaye shi. Yanzu haka, sama da musulmai 5000 dake zaune a kauyuka 6 dake dab da shi suke sallah a masallacin. Domin tunawa da wadannan jajayen sojoji na Red Army, mazauna kauyen Hongguang suka tara kudi don kafa wani karamin dakin tunawa da mazan jiya a cikin masallacin. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China