Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: dandalin FOCAC ya zama jagoran hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da sauran kasashen duniya
2020-01-13 13:20:05        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da ministan harkokin waje da cinikin kasa da kasa na kasar Zimbabwe Sibusiso Moyo a jiya sun gana da 'yan jaridu a birnin Harare na kasar Zimbabwe, inda ya amsa tambayoyi game da nasarorin da aka samu tun bayan da aka kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC da kuma muhimmiyar rawar da dandalin FOCAC ya taka wajen kara inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

Wang Yi ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce da cika shekaru 20 da kafa dandalin FOCAC. A cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, dandalin FOCAC ya kasance wani muhimmin tsarin yin shawarwari da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, inda ya zama jagoran hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da sauran kasashen duniya. An samu babbar nasara a taron koli na Beijing na dandalin FOCAC na shekarar 2018, inda shugabannin Sin da Afirka suka amince da a raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka, da ma matakan yadda za a raya ta.

Wang Yi ya bayyana cewa, tun bayan da aka kafa dandalin FOCAC an samu nasarori a fannoni da dama a wurare daban daban na kasashen Afirka. A fannin ayyukan more rayuwa, yawan hanyoyin jiragen kasa da motoci da Sin ta gina a kasashen Afirka dukkansu sun zarce kilomita dubu 6, kana an gina mashigogin teku kimanin 20 da manyan ayyukan samar da wutar lantarki fiye da 80, wanda ya sa kaimi ga raya masana'antu a nahiyar Afirka tare da inganta karfin raya Afirka da kanta. A fannin kyautata zaman rayuwar jama'a kuwa, Sin ta taimaka wajen gina asibitoci fiye da 130, da filayen wasanni 45, da makarantu fiye da 170, kana ta horar da kwararrun kasashen Afirka fiye da dubu 200 a fannoni daban daban, wadanda suka ba da gudummawa sosai wajen amfanawa jama'ar kasashen Afirka. A fannin ciniki da zuba jari, yawan cinikin dake tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2019 ya zarce dala biliyan 200, Sin ta kasance babbar abokiyar cinikin kasashen Afirka a shekaru 11 da suka gabata a jere. Yawan jarin da Sin ta zuba a Afirka kai tsaye ya kai dala biliyan 110, kana kamfanonin Sin fiye da 3700 sun zuba jari da gudanar da ayyuka a wurare daban daban na Afirka, wadanda suka sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa a Afirka. A sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ya sa wasu kasashen ketare kara maida hankali ga nahiyar Afirka, inda suka kara samar da damammaki ga bunkasuwar kasashen Afirka.

Wang Yi ya ce, a cikin shekaru 20 da suka gabata, Sin ta kiyaye hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka bisa ka'idojin samun moriya masu dacewa, da yin kokarin samun moriyar juna da bunkasuwa tare. Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar kin tsoma baki a harkokin cikin gidan juna, da yin aiki ba tare da gindaya sharadin siyasa ba, sannan ba ta tilasta kowa yin duk abun da ba ya son yi ba. Sin tana saurara ra'ayoyin Afirka, da girmama burin Afirka, da taimakawa Afirka bisa bukatunsu. A yayin hadin gwiwarsu, Sin da Afirka sun yi kokari tare da samun bunkasuwa tare. An kuma kara maida hankali ga kauyuka a yayin da ake raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, Sin ta tura ma'aikatan lafiya dubu 21, wadanda suka bada jinya kyauta ga al'ummar kasashen Afirka miliyan 220. Kasashe da suke zargin kasar Sin kan alakarsu da Afirka, ba za su iya yin irin wannan aiki ba, wannan shi ne dalilin da ya sa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ya samu karbuwa da yabo a Afirka.

Wang Yi ya kara da cewa, bisa tsarin dandalin FOCAC, za a gudanar da sabon taron dandalin a nahiyar Afirka a shekarar badi. Sin za ta yi kokari tare da kasar dake karbar shugabancin hadin gwiwar dandalin wato Senegal don sauraron ra'ayoyi da shawarwari daga dukkan membobin dandalin FOCAC na Afirka. Za a kara raya dandalin FOCAC bisa ka'idojin tattaunawa tare kan manyan manufofin hadin kai, kafa dandalin hadin kai tare da kuma more nasarorin da aka cimma kan hadin kai don amfanawa nahiyar Afirka da ma duniya baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China