Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Nijer 89 sun rasu sakamakon harin da aka kai wani sansanin sojan kasar
2020-01-13 09:50:03        cri
Gwamnatin kasar Nijer ta sanar a jiya cewa, a kalla sojoji 89 sun rasu sakamakon harin da aka kai wani sansanin soja dake yammacin kasar a ranar 9 ga wata. Kuma daga yau Litinin, 13 ga wata, kasar za ta fara cikakken zaman makoki na tsawon kwanaki 3.

A ranar 9 ga wata ne, wasu dakaru dauke da makamai da ba mu san asalinsu ba, suka shiga sansanin soja na kauyen Chinagodar dake kan yankin iyakar kasar da kasar Mali, inda suka yi musayar wuta da sojojin sansanin. Bisa taimakon da sojojin saman Nijer da na wasu kasashen ketare suka ba su, sojojin sansanin sun yi nasarar fatattakar dakarun.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin kai harin.

Cikin 'yan shekarun nan, kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da na ta'addanci da suke mubaya'a ga kungiyar IS, su kan kai hare-hare a yankunan yammacin kasar Nijer, dake kan iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso, lamarin da ya haddasa mutuwa da jikkatar mutane masu yawa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China