Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara aiki da babban madubi mai hangen nesa na zamani mafi girma a duniya
2020-01-12 17:12:05        cri

Kasar Sin ta fara aiki da babban madubi mai hangen nesa na zamani mafi girma a duniya a jiya Asabar, hakan ya bada damar fara amfani da na'urar bayan gwajin da aka yi na tsawon shekaru 3.

Na'urar zata bada dama ga masana ilmin taurari a fadin duniya sannu a hankali, inda zata samar musu kayan aiki mafi karfi wajen gudanar da ayyukan bincike game da tushen wasu halittu da yadda duniya ke gudana.

Ingancin aikin madubin ya zarce yadda aka tsara, wacce ke sahun gaba a duniya, Shen Zhulin, jami'in hukumar kula da harkokin cigaban kasa da gyare-gyare ta kasar Sin ya bayyana hakan a lokacin taron kaddamarwar wanda aka yi a ranar Asabar.

Bayan kaddamar da na'urar mai suna FAST, za'a yi amfani da ita wajen nazari, kuma ana sa ran za'a gudanar da wasu binciken kimiyya masu yawa nan da shekaru biyu ko uku masu zuwa, inji Jiang Peng, shugaban injiniyoyi masu kula da na'urar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China