Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara tafiye-tafiyen bikin bazara na shekarar 2020
2020-01-10 11:03:13        cri

Yau ranar 10 ga wata ne aka kaddamar da tafiye-tafiyen bikin bazara na gargajiyar kasar Sin a hukumance. Sinawa wadanda ke aiki a wurare daban daban a fadin kasar za su koma gidajensu kafin zuwan bikin, wato ranar 24 ga wata. Yanzu haka kasar Sin ta samu babban ci gaba a bangaren gina layukan dogon jiragen kasa, da hanyoyin mota masu saurin tafiya, a don haka babu wahala Sinawa su koma gidaje cikin sauki.

Da misalin karfe daya saura minti ashirin da tara, na daren ranar 10 ga wata, wato da sanyin safiyar yau Juma'a, jirgin kasa mai lambar K4051 ya tashi daga tashar jiragen kasa na nan birnin Beijing, zai kuma tafi zuwa birnin Nantong dake lardin Jiangsu a kudancin kasar Sin. Fasinjoji sama da 600 suna cikin jirgin domin komawa garinsu. Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa, a baya akwai wahala sosai a sayi tikitin jirgin kasa yayin bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, amma yanzu ya fi sauki, a cewarsa: "Jirgin kasa ya kara sauri, babu wahalar sayen tikiti, muna jin dadi."

Bisa kusantowar bikin bazara, an shirya kayayyakin musamman a cikin taragun jirgin, domin murnar zuwan bikin, inda aka lika takardun da aka yanka da almakashi masu nuna fatan alheri a kan tagogin jirgin, duk wadannan suna sawa fasinjoji sun kara begen iyalansu, wani fasinja ya gaya mana cewa, "Iyayena sun tsufa, shekarun haihuwarsu suna kara yawa, dole ne mu koma gida yayin bikin bazara, domin murnar wannan gagarumin biki tare da su."

An fara tafiye-tafiyen bikin bazara ne tun daga shekarar 1979. A wancan lokaci, Sinawa da yawan gaske su kan bar gidajensu domin yin aiki, ko karatu a sauran biranen kasar, saboda fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, bisa al'adun gargajiyar kasar Sin, idan an samu dama, dole ne Sinawa su koma gida domin saduwa da iyalansu a bikin bazara, daga baya kuma za su dawo biranen da suke aiki, hakan ya sa tafiye-tafiyen mutane ke yawaita a lokaci, irin tafiye tafiyen da ba a taba ganin irinsu ba a fadin duniya.

Alkaluman sun nuna cewa, tun daga shekarar 2012 har zuwa yanzu, adadin tafiye-tafiyen Sinawa yayin bikin bazara na kaiwa biliyan 3 a ko wace shekara.

A halin yanzu, yanayin ya sauya. A baya akwai wahala sosai a sayi tikiti, amma yanzu ana iya sayen tikiti da wayar salula. A baya ma'aikatan tashar jirgin kasa ne suke tantance tikitin fasinja, amma yanzu fasinjoji suna iya shiga jirgin ta hanyar tantance hoton fuska ta na'ura kai tsaye.

Kakakin watsa labarai na tashar jirgin kasar birnin Beijing Xie Jingyi, ya yi mana bayani cewa, bana tashar jirgin kasar Beijing ta dauki matakai a jere, domin samar da hidimomi masu inganci ga fasinjoji, yana mai cewa, "Mun samar da na'urorin tantance hoton fuska guda 30 a kofofin tashar, kana mun samar da wasu hidimomi na musamman ga fasinjojin da suke bukata, misali wurin shayar da nono ga jarirai, har ma mun samar da wurin shayar da nono ga jarirai irin na tafi da gidanka guda biyu."

Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, a cikin tafiye-tafiyen bikin bazara da yawansu ya kai biliyan 3 na bana, fasinjojin da za su shiga babar mota za su kai biliyan 2 da miliyan 500, sai fasinjojin da za su shiga jirgin kasa da za su kai miliyan 440, kana fasinjojin da za su shiga jirgin sama za su kai miliyan 79. Ban da wannan, fasinjojin da za su shiga jirgin ruwa za su kai miliyan 45. An lura cewa, adadin fasinjojin da za su shiga jiragen kasa masu saurin tafiya, da jiragen sama, da motocin gida yana kara karuwa.

Mataimakin babban sakataren hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Zhao Chenxin ya bayyana cewa, hukumomin da abin ya shafa na kasar, za su kara kokari domin kyautata hidimomin da ake samarwa fasinjojin, a cewarsa: "Misali an samar da tikiti ta yanar gizo, babu bukatar karbar tikitin takarda. An kara amfani da tsarin biyan kudin tafiya ta hanyar mota mai sauri wato ETC, kana fasinjoji suna iya kammala aikin zaben wurin zama a jirgin sama da kansu. Ana iya cewa, akwai sauki ga Sinawa su sayi tikiti, da kuma shiga jirgi, saboda suna iya sayen tikiti da wayar salula a ko da yaushe, kuma suna iya shiga jirgi ta hanyar tantance hoton fuska ta na'ura kai tsaye." (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China