Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kara inganta tsarin ba da lambobin yabo na kimiyya da fasaha da nufin bunkasa kirkire-kirkire
2020-01-10 10:10:34        cri
Sin ta kara inganta tsarin ba da lambobin yabo na karrama wadanda suka yi fice a fannonin kimiyya da fasaha, a wani yunkuri na bunkasa kirkire- kirkire, da samar da ci gaba mai nagarta.

Ofishin dake tsara ba da lambobin karramawa na kimiyya da fasaha na kasar Sin, ya ce an kara lambar yabo mafi girma ga wadanda suka taka rawar gani a kimiyya da fasaha, da babbar lambar yabo ta kimiyyar asali, da babbar lambar yabo ta ci gaban kirkire-kirkiren fasaha, da kuma ta kasa da kasa game da hadin gwiwar binciken kimiyya da fasaha.

Cikin shekaru sama da 40, an bawa mutane sama da 100,000 manyan lambobin yabo na kimiyyar asali, da na fannonin kirkire-kirkiren fasaha, da na ci gaban kirkire-kirkiren fasaha. Bisa jimilla, kawo yanzu, baki 'yan kasashen waje 118 daga kasashen duniya 20, da hukumomin kasa da kasa 2, da wata kungiyar kasar waje daya ne, suka lashe lambobin yabon kimiyya da fasaha na kasa da kasa da Sin ke bayarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China