Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan CRI sun kai ziyara wurin da jirgin saman Ukraine ya fadi a kasar Iran
2020-01-09 14:12:02        cri

Da safiyar jiya ne wani jirgin saman fasinja na kamfanin jiragen saman Ukraine, ya fadi a dab da filin jiragen sama na Imam Khomeini dake birnin Tehran na kasar Iran, inda bangaren kasar Iran ya tabbatar da cewa, dukkan fasinjoji 167 da ma'aikata 9 dake cikinsa sun mutu a sakamakon hadarin. Bayan abkuwar hadarin, wakilan gidan rediyon CRI dake kasar Iran sun ziyarci wurin da hadarin ya auku, inda wadanda suka ganewa idanunsu da masu aikin ceto a wurin sun bayyana cewa, sun kadu matuka da ganin yanayin wurin.

Da misalin karfe 6 na safiyar jiya ne wani jirgin saman kamfanin jiragen saman Ukraine samfurin Boeing 737, ya tashi daga filin jiragen sama na Imam Khomeini dake birnin Tehran na kasar Iran, zuwa birnin Kyiv na kasar Ukraine, amma bayan mintoci shida kacal da tashinsa, sai jirgin ya fadi a dab da filin jiragen saman, a sakamakon matsalar na'ura. Wannan hadari yana daya daga cikin manyan hadarori mafi tsanani da suka faru a kasar Iran a cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata.

Meyti wani ma'aikacin tsabtar muhalli ne a kauyen dake dab da wurin da jirgin ya fadi, inda ya ga jirgin saman lokacin da ya kama wuta da sanyin safiyar wannan rana. Ya ce jirgin saman ya rika yo kasa kasa, kafin daga bisani ya fadi. Mutumin ya kasa yin karin bayani game da hadarin, saboda matukar kaduwa da abun da ya gani. Ya ce,

"Na ga jirgin saman na tasowa zuwa kusa da inda nake, daga nan sai ya kama wuta, yana tafiya cikin sauri, kana ya fadi a wannan wuri tare da yin bindiga. Bayan da aka samu labarin hakan, mutane da dama sun taru a wurin. Na zo wurin don tsaftace shi, na ga tarkacen jirgin saman, ban ji dadi ba, na ji tamkar 'yan uwana ne ke cikin jirgin saman, hakan ya kusa sanya ni kuka."

Bayan faduwar jirgin saman, dukkan fasinjoji 167, da ma'aikata 9 dake cikinsa sun mutu. Matukin jirgin saman ya hana jirgin saman ya yi karo da gidajen jama'a, a karshe jirgin saman ya fadi a dab da wani filin wasan kwallon kafa. Fitilun hanyoyin motoci dake dab da filin wasan sun lalace, wannan ya shaida yanayin faduwar jirgin saman. A wurin, an ga baraguzan jirgin saman, da kayayyakin fasinjoji da wuta ta kone, ciki har da takalman yara, da jakar karatu da littattafan karatu, ana ji kauri mai tsanani a sakamakon konewar jirgin kurumus.

Vahid wanda ke zauna a kauyen dake dab da wurin da jirgin saman ya fadi, ya shaida aukuwar hadarin. Game da yanayin faduwar jirgin saman, ya bayyana cewa,  

"Gidana yana kusa da wurin. Na ga jirgin saman ya na kewayawa, mai yiwuwa yana son koma ne filin jiragen sama, ko sauka a wani wuri mai fadi, amma bai samu nasarar hakan ba. Ni da abokaina mun lura da yadda matukin jirgin ya yi kokarin kaucewa faduwarsa a kan gidajen jama'a, maimakon haka ya fadi a wani filin wasan kwallon kafa dake da tazarar mita dari daya ko biyu da gidajen jama'a, sai na ji babbar karar fashewar jirgin saman. Na je kusa amma ban ga mutum ko daya da ya tsira daga hadari ba. Ban ji dadin hakan ba, akwai kananan yara dake cikin jirgin."

Bayan abkuwar hadarin, bangaren Iran ya tura masu bada ceto cikin gaggawa, ciki har da motocin bada jinya 22, da jirgin sama mai saukar ungulu daya, amma babu wanda ya tsira daga hadarin. Bisa jerin sunayen da hukumar zirga-zirgar jiragen saman kasar Iran ta bayar, akwai 'yan kasar Iran 147 a jimillar fasinjojin dake jirgin saman.

Ofishin jakadancin Sin dake kasar Iran ya tabbatar da cewa, babu Sinawa a cikin jirgin saman. Kana mai bada ceto na kungiyar Red Crescent Mohammed Reza, ya bayyana wa 'yan jarida cewa, kasancewar mutane da dama sun mutu a sakamakon hadarin, an kwashe awoyi uku ana aikin tattara gawawwakin mamatan. Ya ce,

"Ni mamban rukuni na uku ne da suka zo wurin. Rukunin farko rukuni ne da ya duba ko akwai mutane da suka tsira daga hadarin. Bayan da ya tabbata babu wanda ya tsira, sai rukunin aiki ya fara shiga wurin, don kwashe gawawwakin mutanen da suka mutu, da neman na'urar adana bayanai ta Black Box na jirgin. Yanzu haka an mika na'urar zuwa rukunin masu bincike, daga baya ana fatan tattara baraguzan jirgin saman da ya kone."

Bayan abkuwar hadarin, kakakin gwamnatin kasar Iran ya nuna juyayi ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hadarin. Daga baya kuma Iran ta sanar da gudanar da zaman makoki na tsawon kwana daya, a ranar 9 ga wannan wata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China