Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba Wanda Zai Ji Dadin Tabarbarewar Yanayi A Yankin Gabas Ta Tsakiya
2020-01-08 20:30:57        cri

Tun bayan rasuwar babban kwamandan sojan Iran Qasem Soleimani, mutane suka yi ta yadawa kan yadda kasar Iran za ta mai da martani ga kasar Amruka. Hakika, bayan da aka ayyana sojojin Amurka a matsayin 'yan ta'adda, a safiyar yau Laraba, kasar Iran ta harba makamai masu linzami da dama kan sansanin sojan kasar Amurka dake kasar Iraki, ta kuma yi ikirarin cewa, harin ya hallaka Amurkawa guda 80.

Rikice-rikicen tsakanin kasar Amurka da Iran suna ci gaba da karuwa. Ko da yake ba mu san mataki na gaba da sassan biyu za su dauka ba, amma muna iya tabbatar da cewa, duk wanda ya aikata laifin da bai dace ba, bangarorin biyu za su ci gaba da mai da martani ga juna, abin da hura wutar yanki a Gabas ta Tsakiya, tabbas babu wanda zai ji dadin wannan lamari.

A matsayin na yanki mai muhimmanci ga duniya, yanayin yankin Gabas ta Tsakiya batu ne mai sarkakiya. Daga yankin gabas ta tsakiya, da yakin Iran da Iraki, da yakin tekun Fasha zuwa yakin Afghanistan da yakin Iraki da ISIS masu yaki da kungiyoyi tsattsauran ra'ayi a wannan karni, ba a daina yaki da tashe-tashen hankalu a wannan wuri ba. Idan sabanin dake tsakanin kasar Amurka ta Iran ya tsananta har ma aka kai ga amfani da makamai, tabbas wadanda ba su san hawa ba balle sauka za su rasa rayukansu sanadiyar yaki, kuma zai yi matukar wahala a cimma burin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Bugu da kari, duniya ta damu matuka kan karuwar sabanin dake tsakanin Amurka da Iran. Yakin Gabas ta Tsakiya karo na 4 da ya haifar da rikicin mai a shekarun 1970, ya durkusar da tattalin arzikin kasashe masu ci gaba, don haka, tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya yana da muhimmiyar ma'ana ga duniya baki daya.

A halin yanzu, kasar Iran ta sanar da cewa, ta kawo kashen yakin kare kanta, kuma ba ta neman tayar da yaki, ya kamata ita ma kasar Amurka ta kai zuciya nesa, ta kuma hanzarta dawo teburin yin shawarwari. Domin abu mai muhimmanci ga dukkan sassa a yanzu shi ne gaggauta shimfida kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China