Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta samu karin inganci a fannin samar da hakkin mallakar fasaha
2020-01-08 11:06:22        cri
Kasar Sin ta samu jerin nasarori cikin sama da shekara 1 da ta gabata, wajen samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da kirkire kirkire da samar da ingancin hakkin mallakar fasaha.

Daraktan hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta kasar, Shen Changyu ne ya bayyana haka, yayin taron shugabannin hukumomin kula da hakkin mallakar fasaha, da ya gudana ranar Litinin a nan birnin Beijing.

A shekarar 2019, kasar Sin ta bada izinin kirkire kirkire 13.3 cikin kowane rukuni na mutane 10,000. Jimilar adadin tamburan kasuwanci da aka yi wa rajista, ta zarce miliyan 25, inda cikin harkokin kasuwanci 4.9, 1 ke da tambarin mai rajista.

An kuma kara ingancin jarabawar neman izinin kirkire kirkire. Haka zalika an rage lokacin da ake dauka na samun izinin zuwa watanni 17.3, kuma matsakaicin lokacin registar tambura ya tsaya kan watanni 4 da rabi.

Karfin kirkire kirkire na kasar Sin ne ke kan gaba a duniya. A cewar kididdiga kan harkokin kirkire kirkire na duniya na shekarar 2019 da hukumar kare hakkin mallakar fasaha ta duniya ta fitar, kasar Sin ta matsa gaba zuwa mataki na 14, cikin kasashen duniya masu samun matsakaicin kudin shiga. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China