Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da dokar tabbatar da biyan albashi ga ma'aikata 'yan ci ranin kasar
2020-01-08 09:24:22        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya sanya hannu kan dokar tabbatar da biyan albashi yadda ya kamata ga ma'aikata 'yan ci ranin kasar, tare da tanadin hukunta wadanda suka karya dokar.

Dokar ta majalissar gudanarwar kasar Sin, za ta fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa. Ta kuma kunshin wajibcin biyan ma'aikata 'yan kwadago dake fitowa daga sassan karkarar kasar zuwa birane domin yin aikin karfi, cikakken albashin su a kan lokaci.

Kaza lika ta fayyace nauyin dake wuyan masu daukar ma'aikatan aiki, da ma na sassan hukumomin gwamnati da ma'aikatu. Kana ta yi karin bayani game da dokokin aiki a wasu sassa na musamman, da karfafa fannin sa ido kan hakan.

Sassan dokar sun kuma wajabta biyan 'yan kwadago da tsabar kudi, ko ta asusun banki, sabanin wani nau'in kaya ko takardun lamuni.

Har ila yau, dokar ta ce dole ne a tanadi isassun kudade domin gudanar da ayyukan hukuma, a maimakon 'yan kwangila su dauki nauyin fara biyan ma'aikata da kan su. Dokar ta kuma tanaji hukunci ga jami'an gwamnati da suka tara bashin hakkokin 'yan kwadago.

A daya bangaren kuma, dokar ta umarci daukacin sassan gwamnatin kasar, da su karfafa dokokin aiki, ciki hadda tsara jadawalin bashin da ma'aikata ke bi, su kuma samar da hukunce hukunce na bai daya, ga wadanda suka sabawa dokokin biyan 'yan kwadago hakkokin su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China