Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Saurin Birnin Shanghai" Yana Janyo Hankulan Kasa Da Kasa
2020-01-07 19:53:22        cri

A yayin da kamfanin Tesla na kasar Amurka ya cika shekara daya da kafa reshensa a birnin Shanghai na kasar Sin, a yau Talata, kamfanin Tesla ya sanar da fara aiwatar da shirin Model Y kirar kasar Sin a hukumance a birnin Shanghai, a sa'i daya kuma, ya mika rukunin farko na motoci 3 kirar kasar Sin ga masu sayayya na kasar Sin. Shugaban kamfanin Elon Musk ya bayyana cewa, lalle saurin birnin Shanghai ya burge shi matuka!

Injiniyoyin kasar Sin da dama sun yi nazari da kuma sarrafa manyan na'urorin masana'antun Tesla, wadanda kuma suke kan gaba wajen samar da kayayyaki masu inganci, lamarin da ya nuna ci gaban kasar Sin a harkokin masana'antun kasa da kasa. A halin yanzu, kamfanonin kasashen waje da dama suna ci gaba da kara amincewa da fasahohi da masanan kasar Sin. Kana, manyan kasuwannin da ake da su a nan kasar Sin, da karuwar bukatun al'ummomin kasar suna janyo hankulan kasa da kasa.

Bugu da kari, kasar Sin tana mai da hankali kan bude kofa ga waje ta fuskar manufofi, domin habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen duniya yadda ya kamata. A halin yanzu, ana fuskantar matsalar kariyar ciniki, kasuwanni masu kyau da kasar Sin take da su, da matakan bude kofa ga waje da kasar Sin ta dauka, dukkansu suna karfafa aniyar kamfanonin kasashen ketare wajen zuba jari a kasar Sin cikin dogon lokaci. Tabbas, kasar Sin dake ci gaba da bude kofarta ga waje za ta samar wa kamfanonin ketare kyawawan damammaki na zuba jari. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China