Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar nuna wasan fasaha ta Huaxing ta shimfida gadar cudanya a tsakanin al'ummun Sin da Najeriya
2020-01-07 14:45:32        cri

Tarayyar Najeriya da Sin na hadin gwiwa sosai a fannonin daban daban a halin yanzu, har ma dimbin Sinawa da ke zaune a Najeriya na kokarin kara fahimtar jama'ar kasashen biyu ta hanyar cudanyar al'adu. A birnin Lagos, wanda ya kasance cibiyar tattalin arzikin Najeriya, kuma birni mafi girma a yammacin Afirka, akwai wata kungiyar nuna wasan fasaha mai suna Huaxing, wadda yawancin mambobinta ma'aikatan masana'antu ne. Yanzu suna shimfida gadar cudanyar al'adu a tsakanin al'ummun Sin da Najeriya ta hanyar nuna wasan rawa na Loong da zaki, da wakoki da raye-rayen Sinawa, da ma wasan Kongfu na Sin.

A da, kungiyar nuna wasan fasaha ta Huaxing ta Najeriya wata kungiya ce ta nuna wakoki da raye-raye ta kasar Sin, wadda Mr. Ni Mengxiao da ya raya masana'antar samar da takalma da filayen gona a Lagos ya kafa. 'Yan wasan kuwa matasan Najeriya ne da ke aiki a masana'antarsa.

Yayin da ya tabo magana kan yadda matasan ke sha'awar wasannin fasaha na gargajiyar Sin, Mr. Ni ya bayyana cewa,

"Dukkansu ma'aikata na ne, a lokacin farko, yayin da suke ci gaba da aiki har bayan lokacin tashi, ma'aikata Sinawa kan watsa wasu wakokin kasar Sin. Sannu a hankali kuma, wasu ma'aikata 'yan Najeriya sun iya, kuma sun fara rerawa. Daga baya kuma, mun kafa wata karamar kungiyar wake-wake da raye-raye a cikin masana'antarmu, domin nuna wasannin fasaha na Sin a yayin bukukuwa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne da gaske suna sha'awar wasan Kongfu, da raye-raye, da kide-kide, da wake-wake, da ma al'adunmu."

Bayan da kungiyar ta sha nuna wasa a wurare daban daban, ta shahara sannu a hankali. A watan Afrilu na shekarar 2017, an kafa kungiyar nuna wasan fasaha ta Huaxing a Najeriya a hukumance, wadda wata kungiyar jin dadin jama'a ce da ta samu izni daga gwamnatin Najeriya. Yanzu kungiyar na da 'yan wasa Sinawa kusan 50, da 'yan wasa na Najeriya fiye da 60. Ban da manyan bukukuwa, bayan aiki, 'yan wasan Najeriya su kan je makarantu don nuna wasan fasaha, a kokarin kyautata cudanyar al'adu a tsakanin Sin da Najeriya. Bugu da kari kuma, kungiyar ta shirya gasannin ba da laccoci na matasan Najeriya, bisa aniyar samar da kudin karatu ga daliban kasar. Mr. Ni Mengxiao ya kara da cewa,

"A cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata, kungiyarmu ta nuna wasannin fasahar har kimanin 150, ciki har da bikin bazarar kasar Sin, da bikin murnar kafuwar kasar Sin, da ma sauran harkokin da Sinawa da ke Najeriya suka shirya. Yanzu muna mai da hankali kan harkar nuna wasan fasaha a makarantu, wanda ya samu karbuwa sosai daga wajen malamai da dalibai. A ganina, ba ma kawai muna yada al'adun al'ummar Sin ba ne, har ma muna sa kaimi ga cudanya a tsakanin al'adun kasashen biyu. Haka zakila ma, muna shirya harkokin jin dadin jama'a a ko wane mako, don mara wa dalibai masu rauni baya wajen samun damar karatu."

Mary Fano mai shekaru 20 da haihuwa ta riga ta yi aiki har na tsawon shekaru uku a masana'antar, yanzu tana taka muhimmiyar rawa wajen raye-raye da wake-wake cikin kungiyar. Mary ta ce,

"Ina sha'awar wake-wake da raye-raye kwarai da gaske, kullum muna farin ciki, ina alfahari da zama wata mambar kungiyar Huaxing. Muna fatan za mu iya nuna abubuwan da muka koya a nan, a sauran kasashe da yankuna wata rana."

Kasancewar ma'aikata 'yan Najeriya sun iya rike da fasahar rawar Loong da zaki ta Sin yadda ya kamata, kungiyar Huaxing ta tura wasunsu zuwa birnin Foshan na kasar Sin, don koyon fasahar a cibiyar horar da masu wasan fasahar rawar Loong da zaki ta kasar Sin. Haka kuma yayin da ake nuna al'adun Sin, kungiyar ita ma ta nuna raye-rayen Hausa, da Yarabanci da ma na Igbo, domin nuna hadin gwiwar al'ummar Najeriya da ke da kabilu fiye da 250. Lamarin da ya burge masu kallo na wurin sosai. Mr. Ni Mengxiao yana mai cewa,

"A wani karo, yayin da muke nuna wasan fasaha ga kungiyar mana'antun Najeriya, wani dattijo ya gaya min cewa, ya taba zuwa wurare masu yawa a kasar Sin, da ma kallon wasannin fasahar Sin sau da yawa. Amma abin da ya wuce zatonsa shi ne, yadda 'yan Najeriya ke nuna wasannin fasahar Sin, lallai wani abu ne mai ban mamaki. Ban da wannan kuma, dattijon ya ce, abin da ya fi burge shi shi ne, kungiyarmu ta nuna wasannin fasaha na manyan kabilu uku na Najeriya. Sabo da haka tun daga wancan lokacin, ina da imanin cewa, babu gibi a tsakanin al'adu daban daban, ana iya fahimtar juna sosai ta al'adun."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China