Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sashen sufurin sama na Sin ya samu bunkasuwa a shekarar 2019
2020-01-07 10:21:29        cri
Sashen sufurin jiragen sama na kasar Sin ya samu bunkasuwa a shekarar 2019, kamar dai yadda wani rahoton hukumar dake lura da sashin ya bayyana.

Da yake karin haske game da ci gaban, shugaban hukumar lura da sufurin jiragen sama ta Sin ko CAAC a takaice Feng Zhenglin, ya ce an samu fadadar ayyuka, da karin inganci a bangaren ba da hidima, kana a cikin shekarar ta 2019, adadin fasinjoji da suka yi zirga zirga a kasar ya kai mutum miliyan 660, wanda hakan ke nuna karuwar kaso 7.9 bisa dari a shekara guda.

Feng Zhenglin, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin taron sanin makamar aiki na shekarar 2020 da hukumar ta CAAC ta gudanar. Ya kuma ce adadin hajoji da mutane da aka yi sufurin su a fannin zirga zirgar jiragen sama cikin wannan shekara, ya kai tonne-kilomita biliyan 129.3, yayin da fannin dakon kaya kadai ya kai tan miliyan 7.53, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 7.1 bisa dari cikin shekara guda.

Hukumar CAAC ta ce fannin sufurin sama na Sin, ya samu manyan sauye sauye, inda yawan sabbin hanyoyin sufurin na sama suka karu da kilomita 9,275, baya ga karin sabbin filayen jiragen sama 238.

Bugu da kari, ingancin hidimomi a fannin ya karu, har ma rahoton hukumar ya nuna cewa, a shekarar ta badi, rashin samun jinkiri na tashin jirage ya kai kaso 81.65 bisa dari, a gabar da yawan jiragen da ke tashi suka karu da kaso 5.57 bisa dari a shekara guda. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China