Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya Kamata A Daina Yake-yake
2020-01-06 20:14:46        cri

Sabanin dake tsakanin kasar Amurka da kasar Iran yana da dogon tarihi, hallaka babban kwamanda Qasem Soleimani da kasar Amurka ta yi, ta sake tsananta sabanin dake tsakanin Amurka da Iran.

Tarihi ya nuna mana cewa, duk wanda ke son cimma burinsa ta hanyar daukar matakan soja da matsawa wani ko wata lamba, ba zai cimma nasara ba. Tun lokacin da rikice-rikice suka barke a yammacin Asiya da arewacin Afirka, ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya, wasu dakarun dake adawa da gwamnati wadanda suke samun goyon baya daga kasashen yammacin duniya suna ci gaba da bata tsarin kasa da kasa. Kuma wanzuwar kungiyar mai tsatsauran ra'ayi ta IS ta nuna gazawar manufar kasar Amurka kan aikin yaki da ta'addanci.

Dangane da haka, kasar Iran, wadda ake dauka a matsayin muhimmiyar kawar kasar Syria ta karfafa hadin gwiwarta da gwamnatin kasar Syria da ma wasu kasashen duniya ta fuskar yaki da ta'addanci. A sa'i daya kuma, kasar Iran ta karfafa tasirinta a duniya. A watan Afrilu na shekarar 2019, kasar Amurka ta sanya kungiyar IRGC ta kasar Iran cikin jerin kungiyoyin ta'addanci, domin kara matsa wa kasar Iran lamba, lamarin da ya kawo tabarbarewar dangantaka a tsakanin kasashen biyu.

Hakan ya sa, aka bata yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran wadda aka kulla tsakanin kasar Iran da sauran kasashe 6 a watan Yuli na shekarar 2015 bisa dukkan fannoni. Sa'an nan, kasar Amurka ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar a watan Mayu na shekarar 2018, daga bisani kuma, yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran ta sake gamuwa da matsaloli.

Bayan rasuwar Qasem Soleimani, a jiya Lahadi, gwamnatin kasar Iran ta sanar da shiga mataki na 5 wajen dakatar da wasu tanade-tanade dake cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, wanda ya kasance mataki na karshe ke nan. Amma, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, ko da kasar Iran ta daina aiwatar da wasu tanade-tanadan yarjejeniyar, amma kasar Iran ta kai zuciya nesa.

Yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya ya shiga cikin mawuyacin hali, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su ba da gudumamwa domin kiyaye kundin tsarin mulkin MDD da babbar ka'idar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma gaggauta dawowa teburin yin shawarwari, domin ganin yankin Gabas ta Tsakiya bai shiga cikin sabon rikici ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China