Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin firaministan Sin ya jaddada muhimmancin kawar da talauci a kan lokaci
2020-01-06 09:17:39        cri

Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua, ya yi kira da a kara azama, wajen tabbatar da kammala ayyukan da aka tsara na kawar da talauci daga yankunan karkara, da gundumomi, bisa mizanin da aka amince da shi.

Hu, wanda kuma shi ne jagoran majalissar gudanarwar kasar ta ayyukan yaki da fatara da samar da ci gaba, ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, yayin wani taro na musayar ra'ayi da ya gudana a yankin Nujiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Mataimakin firaministan kasar ta Sin, wanda ya tabbatar da fara aiki gadangadan a wannan fanni, ya ce akwai bukatar cimma nasarar a zo a gani a yaki da fatara, don haka ya dace a aiwatar da matakai na hakika domin dakile manyan kalubale, ta yadda za a kai gaci a wannan muhimmin aiki.

Daga nan sai ya jaddada muhimmacin aiwatarwa, da karfafa tallafin da ake baiwa yankuna mafiya fama da fatara cikin dogon lokaci, ciki hadda bunkasa ci gaban masana'antu, da daidaita samar da guraben ayyuka a yankuna mafiya fama da talauci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China