Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangaren manhajar na'ura mai kwakwalwa ta kasar Sin ta bunkasa a watanni 11 na shekarar 2019
2020-01-05 15:15:00        cri
Wata kidddiga daga hukumonin kasar Sin sun nuna cewa fannin manhajoji na kasar Sin ya yi matukar samun bunkasuwar kudaden shiga da karuwar riba a farkon watanni 11 na shekarar da ta gabata.

Baki dayan kudaden shigar da wannan fanni ya samu ya tasamma RMB yuan triliyan 6.46 kwatankwacin dala biliyan 922.9 daga watan Janairu zuwa Nuwamba, inda ya karu da kashi 15.5 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2018, kamar yadda ma'aikatar kula da masana'antu da fasahohin zamani ta kasar Sin ta bayyana.

Haka zalika, yawan ribar da aka samu ya karu da kashi 11 bisa 100, ya zarta na makamancin lokacin shekarar 2018 wanda ya kai RMB yuan biliyan 826.

Adadin manhajojin da aka sayar da su a ketare ya karu da kashi 3.4 bisa na makamancin shekarar 2018 wanda ya kai dala biliyan 42.2.

Bisa alkaluman, kayayyakin manhajoji na fasahohin zamani da aka yi cinikinsu sun bunkasa kudin shigar kasar Sin da kashi 13.8 da kuma kashi 17 bisa 100. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China