Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na burin kara kilomita 2,000 na layukan dogo masu saurin tafiya a 2020
2020-01-04 16:38:18        cri

Kasar Sin na shirin kara hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya kilomita 2,000 a bana.

Kamfanin kula da layukan dogo na kasar Sin, ya ce ya zuwa karshen 2019, jiragen kasa masu saurin tafiya, sun yi tafiyar da ta kai kilomita 35,000, adadin da ya karu da sama da kilomita 5,000 akan na shekara guda da ta gabata, kuma ya dauki kusan kaso 70 na jimilar ta duniya baki daya.

Ya ce kasar na shirin fadada layukan dogo da kilomita 4,000 a bana, a kan kilomita 139,000 da ake da su ya zuwa karshen 2019.

Kamfanin ya kara da cewa, jarin da gwamnati ta zuba a bangaren a 2019, ya kai yuan biliyan 802.9, kwatankwacin dala biliyan 115.19, sai dai, bai bayyana jarin da za a zuba a bana ba.

Ana sa ran fasinjoji za su yi tafiye-tafiyen da adadinsu ya kai biliyan 3.85 ta jiragen kasa a bana, adadin da ya karu a kan biliyan 3.57 na 2019. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China