Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar New York Times ta sake yada kalaman harzuka jama'a kan batun Xinjiang
2020-01-03 19:44:29        cri

Kwanan baya jaridar "The New York Times" ta Amurka, ta wallafa wani rahoto, inda a ciki aka bayyana cewa, gwamnatin yankin Xinjiang ta kasar Sin, tana tilastawa mazauna yankin 'yan kananan kabilu, har da 'yan kabilar Uygur, su yi aiki domin kyautata hallayarsu. To sai dai kuma wannan zargi da jaridar ta yiwa kasar Sin, ba shi da dalili ko kadan, kuma yunkuri ne kawai na shafawa gwamnatin yankin kashin kaza. Ko shakka ba bu, rahoton bai shafi samar da labarai ba, almara ce kawai da aka rubuta bisa tunanin kashin kai.

A cikin shekaru biyar da suka gabata, mazauna yankin Xinjiang da yawansu ya kai miliyan 2 da dubu 314 da dari 7, sun kubutar da kansu daga kangin talauci, ta yadda adadin masu fama da talauci ya ragu daga kaso 22.84 bisa dari a farkon shekarar 2014, zuwa kaso 6.51 bisa dari a yanzu. Misali, a yankin Kashgar, adadin marasa aikin yi, wadanda suka yi rajista ya ragu zuwa kaso 2.4 bisa dari a shekarar 2018.

Amma rahoton da jaridar "The New York Times" ta Amurka ta wallafa, bai gabatar da abubuwan dake shafar kyautatuwar yanayin rayuwa a yankin ba ko kadan, maimakon haka sai ya rubuta cewa, mazauna yankin 'yan kananan kabilun kasar Sin, sun samu aikin yi ne saboda gwamnatin yankin na tilasta musu, har ma rahoton ya mayar da batun a matsayin wata masifa. A bayyane take cewa, mai rubuta rahoton ba ya so ya ga ci gaba yankin Xinjiang, haka kuma yana fatan mazauna yankin su kasance cikin mawuyacin yanayi. Ana iya cewa, ba shi da manufa ta kirki ko kadan.

Bugu da kari, rahoton ya hada batun da cibiyar horaswar fasahohin sana'o'i dake yankin, inda ya bayyana cewa, bayan da aka horas da mutane, ana tura su zuwa kamfanoni domin su yi aiki a ciki, amma hakika makasudin kafa cibiyar shi ne yaki da ta'addanci, da masu tsattsauren ra'ayi, tare kuma da kyautata rayuwar jama'a.

Ba dai zai yiwu ba a rufe ainihin yanayin da ake ciki, duk da cewa wasu kafofin watsa labarai da 'yan siyasa na kasashen yamma, suna kokarin shafawa yankin Xinjiang kashin kaza, amma duk wanda ya taba zuwa yankin, ba zai amince da ra'ayoyinsu ba.

Yanzu an shiga shekarar 2020, yankin Xinjiang zai cimma burin kawar da talauci daga dukkanin fannoni tare da sauran yankunan kasar Sin, har ma zai kai ga samun wadata. Rahotanni marasa tushe da wasu kafofin watsa labaran kasashen yamma suka wallafa, za su kasance abun dariya ko ma abun kunya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China