Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na gaggauta raya harkokin bada inshora don kula da tsoffi
2020-01-03 13:57:09        cri

Rahotanni daga ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, sun ce bisa shawarar raya harkokin bada inshora a bangaren samar da hidimomin jama'a da kasar ta bullo da su, Sin za ta nuna kwazo wajen raya harkokin bada inshora, don kula da tsoffi ta hanyoyi daban-daban, ta yadda za'a tara kudin inshora da yawansu ya kai Yuan triliyan 6 ga tsoffin da suke da bukata, nan zuwa shekara ta 2025.

A halin yanzu, ana kara samun mutanen da suka manyanta a kasar Sin, inda yawan tsoffin da suka wuce shekaru 60 da haihuwa ya kai miliyan 250, wadanda kuma ke bukatar samun inshora da ta dace.

Shawarar da aka bayar ta kuma ce, ya kamata a gaggauta bude kofar kasuwar bada inshora ga kasashen waje. Daga ranar 1 ga wata, yawan jarin waje dake cikin kamfanonin bada inshora, na hadin-gwiwar jarin gida da na waje, zai iya kaiwa kaso 100.

Har wa yau, shawarar ta bukaci a kyautata harkokin bada inshora mai inganci.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China