Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tafara Mugnara: Ina kokarin sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe
2020-01-03 14:02:56        cri

Kasar Zimbabwe, dadaddiyar abokiyar zumuncin kasar Sin ce, tun lokacin da al'ummomi suka yi gwagwarmayar neman 'yanci a karnin da ya wuce, jama'ar kasashen biyu suka sada zumunci mai karfi a tsakaninsu. A yanzu matasan kasar Zimbabwe da suka iya harshen Sinanci da fahimtar kasar Sin suna karuwa, wadanda ke yada dadadden zumunci a tsakanin kasashen biyu. Tafara Mugnara, wanda ya taba karatu a kasar Sin yana daya daga cikinsu.

"Suna na Tafara, shekaru na 29, na kammala karatu a jami'ar Zimbabwe, kuma na samu digiri na biyu ne a fannin dangantakar kasa da kasa a jami'ar Xiamen ta kasar Sin daga shekarar 2016 zuwa 2019."

Yadda Tafara dan kasar Zimbabwe ke bayyana kansa da Sinanci. A yayin da yake karatu a jami'ar Zimbabwe, ya shafe shekaru uku yana koyon Sinanci a kwalejin Confucious dake jami'ar. A shekarar 2014, ya samu maki mai kyau a jarrabawar koyon Sinanci, har ma ya samu kudin bonas na kwalejin, tare kuma da samun damar yin karatu a kasar Sin. Tafara ya ce, koyon Sinanci ya ba shi damammaki masu yawa, da kuma canja makomarsa. Me ya sa ya koyi Sinanci? Game da wannan tambaya, Tafara ya amsa cewa, saurin ci gaba da kasar Sin ta samu ya sanya ya fahimci muhimmancin koyon Sinanci. Ya ce,

"Yanzu kasar Sin ta kasance rukuni na biyu a duniya a fannin tattalin arziki, ita ce kuma abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen Afirka, don haka iya harshen Sinanci na da muhimmanci kwarai. Ban da wannan kuma, koyon Sinanci zai taimaka wajen fahimtar yanayin siyasa, tattalin arziki da kuma al'adun kasar ta Sin, wannan ma yana da muhimmanci sosai, wadannan su ne dalilan da suka sanya na nemi digiri na biyu a kasar Sin."

A shekarar 2014, Tafara ya koyi Sinanci na shekara guda a jami'ar Renmin ta kasar Sin, daga baya sai ya nemi yin digiri na biyu a jami'ar Xiamen. A cikin wadannan shekaru biyar da ya yi yana zaune a kasar Sin, Tafara ya yi abokai da Sinawa masu yawa, ya kuma ziyarci birane da yawa na kasar. A cewar Tafara, yanayin da yankuna daban daban na kasar ke ciki da yadda zaman rayuwar jama'arsu yake sun burge shi sosai, ga misalin jama'ar lardin Shanxi na sha'awar shan ruwa mai tsami sosai da dai sauransu. Baya ga haka, manyan kayayyakin more rayuwa masu kyau, saukin da aka samu wajen tsarin sufuri, musamman ma saurin ci gaban da kasar ta samu a fannin kimiyya da fasaha, dukkansu sun jawo hankalinsa sosai. Tafara ya ce,

"Birnin da na fi kauna shi ne Shenzhen, a shekaru 30 da suka wuce, Shenzhen bai samu ci gaba sosai ba, wani karamin kauyen kamun kifi ne kawai. Amma yanzu Shenzhen ya kasance wani birni mai ci gaba, shi ne kuma cibiyar kimiyya da fasaha ta kasar Sin. Ana iya cewa, kasar Sin ta samu saurin bunkasuwa ta fuskar kimiyya da fasaha, har ma ta wuce matsayin kasashen Japan, Amurka da Turai a wasu fannoni. Ina fata kasar Zimbabwe za ta yi koyi da kasar Sin a fannin ci gaban kimiyya da fasaha."

A watan Yuli na shekarar 2019, Tafara ya komo kasarsa ta Zimbabwe bayan ya kammala karatu a kasar Sin, ya kuma samu aikin tafinta a wani kamfanin kasar Sin dake wurin. A ganin Tafara, masu fassara sun zama wata gadar yin cudanyar al'adu, sun kuma kasance masu karfafa zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Ta wannan aikin fassara kuma, Tafara ya fahimci muhimmancin hadin kai a fannin tattalin arziki ga kasashen Sin da Zimbabwe matuka.

"Gaskiya kasashen Sin da Zimbabwe aminan juna ne a ko da yaushe. Ina ganin cewa, zuba jari da kamfanonin kasar Sin ke yi a kasar Zimbabwe wani mataki ne na samar da moriyar juna da samun nasara tare ga bangarorin biyu. Mummunan yanayin da kasar Zimbabwe ke ciki, sakamakon yadda kasashen yamma ke sanya mata takunkumi, ya sa inganta hadin kai tare da Sin ya zama wata muhimmiyar hanya ce da za ta taimakawa kasar Zimbabwe wajen farfado da tattalin arzikinta."

Kamar Tafara, akwai daliban kasar Zimbabwe sama da 5000 wadanda suka kammala karatu a jami'o'in kasar ta Sin, yanzu haka suna aiki a Zimbabwe a fannoni daban daban, ciki har da ba da ilmi, al'adu, kiwon lafiya, yin kirkire-kirkire da dai sauransu, suna taka muhimmiyar rawa ga ci gaban kasarsu, da inganta zumunci a tsakanin Sin da Zimbabwe. Yanzu kuma, daliban Zimbabwe fiye da dubu 10 suna karatu a nan kasar Sin, za kuma su kasance sabbin masu yadda zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China