Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba zai yiwu 'yan siyasar ketare su hana ci gaban Sin ta hanyar tsoma baki cikin harkokin HK ba
2020-01-02 19:41:36        cri

Yau gidan rediyon kasar Sin, ya gabatar da wani sharhi mai taken "Ba zai yiwu, wasu 'yan siyasar kasashen waje su hana ci gaban kasar Sin ta hanyar tsoma baki a cikin harkokin yankin musamman na Hong Kong ba."

Sharhin ya bayyana cewa, kwanan baya, wasu 'yan siyasar kasashen waje, sun mika sakon hadin gwiwa ga gwamnar yankin Hong Kong Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, lamarin da ya nuna cewa, wadannan 'yan siyasa sun tsoma baki a cikin harkokin yankin a fili, kuma yunkurinsu shi ne hana ci gaban kasar Sin.

Sharhin ya yi nuni da cewa, zargin da 'yan siyasar suka yi a cikin sakon na su, ba shi da tushe ko kadan, saboda sun soki 'yan sandan yankin Hong Kong, wadanda suke kokarin tabbatar da tsaron yankin bisa ka'ida, kuma sun yi watsi da laifuffukan da masu tada tarzoma suka aikata.

Ko shakka ba bu, an lura cewa suna mayar da baki fari, kuma hakika 'yan sandan yankin Hong Kong suna yin hakuri matuka, yayin da suke gudanar da aikin kiyaye kwanciyar hankali a yankin, amma wadannan 'yan siyasa sun gabatar da shawarar cewa, ya kamata kasa da kasa su kafa wata hukumar bincike mai 'yanci, domin gudanar da bincike kan aikin 'yan sandan yankin Hong Kong. To sai dai kuma Hong Kong yanki ne na kasar Sin, shin ko mene ne dalilin da ya sa hukummomin kasa da kasa za su gudanar da bincike kan harkokin cikin gidan kasar ta Sin?

Sharhin ya jaddada cewa, kasar Sin tana da karfin tabbatar da wadata, da zaman lafiya a yankin Hong Kong, kuma ya dace 'yan siyasar kasashen waje su fahimci yanayin da ake ciki yanzu, su daina tsoma baki a cikin harkokin yankin Hong Kong, kuma ba zai yiwu su cimma yunkurinsu ba, kana tabbas makarkashiyarsu za ta bi ruwa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China