Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Umaro Sissoco Embalo ya lashe zaben shugabancin kasar Guinea-Bissau
2020-01-02 11:07:57        cri
Hukumar zaben kasar Guinea-Bissau (NEC) ta ayyana tsohon firaministan kasar Umaro Sissoco Embalo a matsayin wanda ya lashe zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata.

Sakamakon wucin gadi da hukumar ta fitar jiya Laraba, na nuna cewa, Embalo dan takarar jam'iyar MADEM-G15 ya samu kaso 53.55 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben na ranar 29 ga watan Disamba, yayin da abokin karawarsa na jam'iyyar PAIGC, Domingos Simon Pereira, wanda shi ma tsohon firaministan kasar ne, ya samu kaso 46.45 cikin 100 na kuru'in da aka kada.

Hukumar zaben ta ce, kaso 72.67 cikin 100 na masu zabe ne suka fito kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar, adadin da ya yi kasa da na zagayen farko na zaben.

Masu kada kuri'a 761,676 ne suka fito zaben na ranar Lahadi, inda suka kada kuri'u a tashoshin zabe 3,139 da aka tanada a sassan kasar da ma kasashen waje. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China