Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na yin iya kokarin daidaita matsalolin da ake fuskanta a duniya
2019-12-31 22:01:27        cri

Yau Talata ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya ba da sharhi, inda ya ce, a shekarar 2019 dake dab da karewa, ana fama da yunkurin dakatar da dinkuwar duniya baki daya, tare da fuskantar matsaloli a fannonin tafiyar da harkoki, da amincewa juna, da zaman lafiya da ci gaba.

A matsayinta na rukuni na 2 a duniya ta fuskar tattalin arziki, kasar Sin ta burge mutane sosai wajen tabbatar da dinkuwar duniya baki daya, ta fuskar tattalin arziki da daidaita matsalolin tafiyar da harkoki, da amincewa juna, da zaman lafiya da ci gaba.

Sharhin ya ce, a shekarar 2019, tunanin kasar Sin na tafiyar da harkokin duniya ta hanyar yin shawarwari tare, da bunkasuwa tare, da kuma cin moriya tare, ya taimaka wajen daidaita matsalar tafiyar da harkokin kasa da kasa yadda ya kamata. Kasar Sin na tsayawa kan yin adalci da karbar kowa, kana hanyar da take bi wajen raya kasa yadda ya kamata don amfanar kowa ta sanya al'ummomin duniya su ci gajiyar ci gaban dinkuwar tattalin arzikin duniya,

Bugu da kari, sharhin ya jaddada cewa, ko da yake ana shan fuskantar matsaloli wajen raya hulda a tsakanin bangarori 2, tsakanin bangarori daban daban da kuma a wasu yankunan duniya, amma jama'ar Sin ba za ta ji tsoron komai ba, za ta jure wahala, za ta kuma samu sabon ci gaba, a kokarin kara ba da tabbaci a duniyarmu maras tabbaci. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China