Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 23 sun mutu sakamakon harin da aka kai a gabashin Kongo Kinshasa
2019-12-31 13:54:59        cri

Wani jami'i a lardin arewacin Kivu na kasar Kongo Kinshasa ya shedawa kafar yada labarai ta kasar cewa, an kai hari a lardin dake gabashin kasar, a daren ranar 29 zuwa safiyar ranar 30 ga wata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 23.

Jami'ai da hukumomin tsaron Congo sun nuna cewa, dankarun ADF dake adawa da gwamnati sun kaddamar da hari a daren ran 29 ga wata tare da cinna wuta a gidaje da dama.

Tun lokacin sojojin gwamnatin Kongo Kinshasa suka kaddamar da matakan murkushe haramtattun dankarun a gabashin kasar a karshen watan Oktoba na bana, hakan ya sa wadannan dankaru ciki hadda ADF suke mayar da martini kan fararen hula. Alkaluman da aka fitar na nuna cewa, fararen hula fiye da 200 ne suka rasa rayukansu a irin wadannan hare-hare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China