Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A wannan shekara, huldar Sin da Rasha ta shiga sabon zamani
2019-12-30 14:24:45        cri


Shekarar 2019 da ke dab da karewa,shekaru ke nan 70 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Rasha. A wannan shekara, shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da takwaransa na kasar Rasha, Viladimir Putin suka rattaba hannu kan hadaddiyar sanarwa, wadda ta daukaka huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. A wannan shekarar ce kuma, shugabannin biyu su ka kalli yadda aka fara aikin shimfida bututun iskar gas mafi tsayi a duniya, wanda kasashen biyu suka yi cikin hadin gwiwa.

Idan an waiwayi shekarar 2019, za a ga irin dimbin nasarorin da kasashen biyu suka cimma wajen raya huldarsu. A watan Afrilun shekarar ta 2019, an gudanar da ganawar farko a tsakanin shugaba Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin. A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya bayyana huldar kasashen biyu kamar haka,"Bana shekaru 70 ke nan da kafa jamhuriyar jama'ar Sin, haka kuma shekaru 70 ke nan da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Rasha. A cikin wadannan shekaru 70 da suka wuce, duk da wahalhalun da suka fuskanta, kasashen biyu sun kai ga daukaka huldarsu zuwa wani babban matsayi ta fannonin amincewa da juna, da hadin gwiwa da juna, da kuma manyan tsare-tsare."

Baya ga haka, jami'ar Tsinghua ta kasar Sin ta kuma ba wa shugaba Putin digirin girmamawa, abin da shugaban ke yin alfahari da shi, a sabo da yadda abokin arzikinsa Xi Jinping ma ya taba dalibta a jami'ar. Yana mai cewa, "Babban abin alfahari ne gare ni da jami'ar Tsinghua ta ba ni digirin girmamawa, jami'ar da ta kasance daya daga cikin jami'o'i mafiya muhimmanci a kasar Sin, kuma cibiyar ilmantarwa da nazari da ke tasiri a fadin duniya. Da dama daga cikin fitattun masana da 'yan siyasa na kasar sun yi karatu ko aikin koyarwa a wajen. Daga cikin daliban da suka kammala karatunsu a jami'ar, akwai abokin arzikina shugaba Xi Jinping na kasar ta Sin."

Wata guda bayan ganawar, shugaba Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kasar Rasha, ziyarar da ta kasance ta farko tun bayan da ya sake zama shugaban kasar Sin. Baya ga ganawa da takwaransa na Rasha, shugaba Xi Jinping ma ya karbi digirin girmamawa daga jami'ar Saint Petersburg ta kasar Rasha.

 

Ziyarar ta zo daidai a lokacin da kasashen biyu ke murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu. A lokacin ziyarar, shugabannin biyu sun kuma rattaba hannu kan hadaddiyar sanarwar raya huldar abokantaka ta hadin gwiwa da manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni cikin sabon zamani da ma yadda za a inganta zaman karko a fadin duniya a yanayin da ake ciki, sanarwar da ta kara daukaka huldar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A kokarin da shugabannin kasashen biyu suka yi, an cimma gaggaruman nasarori a wajen raya huldar kasashen biyu. A farkon wannan watan da muke ciki, ta kafar hoton bidiyo shugabannin biyu sun gane ma idonsu yadda aka fara aiki da bangaren gabashi na bututun iskar gas da aka shimfida tsakanin kasashen biyu. Bututun da ke da tsawon kilomita sama da 8000 ya ratsa wasu larduna 9 na kasar Sin, zai kuma amfana wa al'ummar kasar Sin dake sassan arewa maso gabas da mashigin tekun Bohai da sauransu. Shugaba Xi Jinping yana mai cewa,"A cikin shekaru sama da biyar da suka wuce, sassan da aikin ya shafa na kasashen biyu sun aiwatar da hadin gwiwa yadda ya kamata, magina bututun sun tinkari wahalhalun da dama, kuma daga karshe sun kammala aiki cikin inganci, wadanda suka nuna wa duniya kwarewarsu da kuma nasarar hadin gwiwar kasashen biyu. Ina fatan sassan biyu za su ci gaba da kokari, don su kara samar da ingantattun ayyuka irin wannan, domin kara amfanawa al'ummar kasashen biyu." (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China