Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahohin Sin Sun Taimakawa Duniya Wajen Yaki Da Talauci
2019-12-29 20:02:43        cri
A shekarar 2019, Sin ta sake cimma burin rage yawan masu fama da talauci da fiye da miliyan 10, ana sa ran cewa, an kawar da talauci da kashi 95 cikin dari na masu fama da talauci. Sin tana kokarin cimma burin kawar da talauci a dukkan kasar da raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi a dukkan fannoni.

An yi nuni da cewa, akwai mutane fiye da miliyan 700 dake fama da talauci a duniya a halin yanzu. Sin ta dauki matakin yaki da talauci ta hanyoyin raya sana'o'i, da daukar kwararan matakai na yaki da talauci da sauransu, wadanda suka kawo fasahohin yaki da talauci ga sauran kasashe masu tasowa, kuma kasa da kasa sun amince da su. Kana Sin ta samar da gudummawa ga sauran kasashe masu tasowa ba tare da gindaya sharadin siyasa ba. Sai dai Sin ta kara yin hadin gwiwar samun moriyar juna yayin da ake aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje, da taimakawa sauran kasashe masu tasowa wajen inganta karfinsu na samun bunkasuwa mai dorewa. Bisa rahoton bincike da bankin duniya ya gabatar, an ce, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta taimakawa kasashe masu bin ta wajen kawar da masu fama da talauci mai tsanani da yawansu ya kai miliyan 7 da dubu 600, da kuma mutane miliyan 32 sun warware matsalar talauci da suke fuskanta. An koyi fasahohin da Sin ta samu wajen yaki da talauci a duk duniya, wannan ya shaida cewa, Sin wata babbar kasa mai tasowa ce da ta sauke nauyi dake bisa wuyenta wajen sa kaimi ga yaki da talauci a duniya.

An jaddada cewa, Sin za ta cimma burin samun zaman al'umma mai matsakaicin karfi a dukkan fannoni a shekarar 2020, za a warware matsalar fama da talauci da wasu mutane ke fuskanta, wadanda kudin shigar su ba su iya biyan bukatun zaman rayuwarsu. Hakan zai shigar da fasahohin Sin a tarihin yaki da talauci na dan Adam, kana zai sa kaimi ga kasa da kasa da su yi imani da yaki da talauci, da samar da muhimmiyar gudummawa wajen yaki da talauci da samun bunkasuwa mai dorewa a duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China