Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aikin kirkire-kirkire ne sabon karfin ci gaban kasar Sin
2019-12-28 16:58:24        cri

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice ya fitar da wani sharhi yau Asabar, mai taken "Aikin kirkire-kirkire ya zama sabon karfi na ci gaban kasar Sin gami da sabon zarafi ga duniya".

A cewar sharhin, an yi nasarar harba roka mai suna Long March-5 a daren jiya Jumma'a, wadda ita ce sabuwar roka mai dauke da taurarin dan Adam mafi girma a kasar. Haka kuma a jiya, an bayyana yadda tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 wato BDS-3 ke samar da hidimomi ga kasashe da yankunan duniya a shekara daya, inda aka nuna cewa, tsarin na Beidou ya shiga wani sabon zamani na harkar hidimar kasa da kasa a shekara ta 2019.

Kasar Sin ta bayyanawa duniya wadannan manyan nasarori biyu da ta samu a bangaren kimiyya da fasaha a tsawon yini guda, al'amarin da ya shaida cewa, kasar ta samu karin ci gaba a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, har ya kasance sabon kuzari ga bunkasuwar kasar mai inganci, wanda ya samar da sabon zarafi ga habakar tattalin arziki gami da ci gaban kimiyya da fasaha na al'ummar duniya baki daya.

Sharhin ya jaddada cewa, yin kirkire-kirkire shi ne babban dalilin da ya sa kasar Sin ta iya samun ci gaba mai dorewa. A cewarsa, a shekarar da ta kusan karewa wato 2019, kasar Sin ta yi kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha har ta samu dimbin nasarori a fannoni da dama, ciki har da nazarin tushe, da muhimman ayyuka da kuma ayyukan zaman rayuwar al'umma. Tsayawa kan aikin yin kirkire-kirkire bisa karfin kanta, da kokarin halartar ayyukan yin kirkire-kirkire na duniya, ya sa kasar Sin take kara bada gudummawarta ga ci gaban harkokin duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China