Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shin kun san yadda ake yin karya kan batun jihar Xinjiang?
2019-12-27 20:46:28        cri

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice ya fitar da wani sharhi yau Jumma'a mai taken "Shin kun san yadda ake yin karya kan batun jihar Xinjiang?"

Sharhin ya ce, wata tashar Intanet mai zaman kanta ta kasar Amurka mai suna "Grayzone" ta wallafa wani bayani, inda ya tona asirin wasu mutane da cibiyoyi masu kyamar kasar Sin wadanda suka yayata labaran karya kan batun jihar Xinjiang. Hakan zai taimakawa kasashen duniya kara fahimtar ainihin halin da ake ciki a jihar, tare kuma da tona asirin wasu 'yan kasashen yammacin duniya da suka tsani kasar Sin wadanda ake hada baki da su don shafawa gwamnatin kasar kashin kaji.

A cewar sharhin, bisa binciken da Grayzone ta yi, abun da kafofin watsa labaran yammacin duniya ke cewa wai an kame miliyoyin musulmi a jihar Xinjiang ta kasar Sin ba shi da tushe balle makama. Alal misali, wata cibiya mai suna "Network of Chinese Human Rights Defenders (CHRD)" ta zanta da 'yan kabilar Uygur takwas kawai, amma har ta iya bayyana cewa an cafke musulmi masu tarin yawa a Xinjiang. Har wa yau akwai wani mai suna Adrian Zenz, wanda a cewarsa shi "mai fada-a-ji" ne, ya yi irin wannan furuci bisa ga wani rahoton da ya karanta a wata kafar yada labarai ita kadai. Gaskiyar labarin shi ne, a bayan irin wadannan cibiyoyi ko mutane ma, akwai wata hukuma ta Amurka, wato hukumar leken asirin kasar ko kuma CIA a takaice.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China