2019-12-26 20:35:56 cri |
Sharhin ya ce, a shekarar dake dab da karewa wato 2019, bude kofa ga kasashen waje wani muhimmin fanni ne na ci gaban kasar Sin, wanda kuma dalili ne da ya sa kasar Sin take iya kara samarwa duniya alheri.
A cewar sharhin, a bana, yayin da ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci da ra'ayin nuna bangaranci ke ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya, kasar Sin na ci gaba da zurfafa bude kofarta ga kasashen waje a fannonin musayar kayayyaki da inganta ka'idoji, da kara samun kwarewa domin tinkarar hadari da kalubale. Kasar Sin dake fadada bude kofarta ga kasashen ketare na kara samar da alheri da moriya ga duk fadin duniya.
Har wa yau, sharhin ya ce, a sabon zamanin da muke ciki, ya kamata Sin ta fadada bude kofar kasuwanninta, da kyautata yanayin kasuwanci, da zurfafa hadin-gwiwar bangarori daban-daban, da ci gaba da inganta ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya", a wani mataki na sanya sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China