Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kashe dala biliyan 80 wajen tallafawa alummun dake cikin bukata daga 2016 zuwa yanzu
2019-12-26 09:42:47        cri

Ma'aikatar lura da al'amuran al'umma ta kasar Sin, ta ce daga shekarar 2016 zuwa yanzu, kasar ta kashe yuan biliyan 561.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 80, don tallafawa al'ummu daban daban dake cikin tsananin bukata.

Wani rahoto da ma'aikatar ta fitar a jiya Laraba, ya nuna cewa an yi amfani da irin wadannan kudade wajen tallafawa masu fama da tsananin talauci, da marayu, da marasa matsuguni da dai sauransu.

Ministan lura da harkokin jama'a Li Jiheng, shi ne ya gabatar da rahoton ga zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin domin tattaunawa, yayin taro daya da yake gabatarwa a duk watanni 2, wanda a wannan karo ke gudana tsakanin ranekun 23 zuwa 28 ga watan Disamba.

Li ya ce Sin na dukufa wajen samar da managarcin tsarin tallafawa al'umma, wanda amfaninsa ke kara bayyana a fili.

Ministan ya ce ma'aikatarsa, ta sha alwashin bunkasa cin gajiya daga albarkatun al'umma, a nan gaba za ta kuma fadada sanya ido, da goyon bayan samar da dokokin tallafawa al'umma yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China