Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin Yada Labarai Na Birtaniya Sun Ba Da Labari Kan Gidan Kurkukun Shanghai Bisa Tunaninsu
2019-12-25 13:31:42        cri
Kwanan baya, kafofin yada labarai na kasar Birtaniya sun zargi gidan kurkuku na Qingpu dake birnin Shanghai n kasar Sin da cewa, yana tilastawa masu laifi 'yan asalin kasashen ketare da su samar da katin murna na Kirismeti. Babban gidan rediyo da telibijin kasar Sin CMG ya zanta da shugaban wannan gidan kurkuku Li Qiang, wanda ya ce, labaran da kafofin suka bayar ba shi da wata hujja.

Li Qiang ya gayyawa manema labarai cewa, ana sauya halin wadanda suka aikata laifi ta hanyar sanya su yin ayyuka da zummar kara fasahohinsu, don sun iya kama aiki bayan sun fita daga gidan kurkuku. Na farko, ba a tilasta musu. Na biyu, masu laifin suna iya zabar ko za su yi ko ba za su yi ba. Ayyukan da za su iya zaba sun hada da sassakar duwatsun jade masu daraja, da aikin dinki, da aikin samar da abubuwan wasa na takardu da dai sauransu.

Idan masu laifi na son yin irin wadannan ayyuka, za su samu kudin shiga, domin fara sabuwar rayuwa bayan sun fita daga kurkuku, kana sauran kudin suna iya sayen abubuwan yau da kullum, da tuntubar iyalansu yayin da suke cikin gidan kurkuku. Peter Hamphrey da Jaridar Sunday Times ta ambata, fursuna ne da aka daure shi cikin gidan kurkukun daga shekarar 2013 zuwa 2015. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China