Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Sin da Masar sun sanya hannu kan yarjejeniyar gina katafaren kamfanin samar da sinadarin phosphoric Acid
2019-12-25 10:35:44        cri

Kamfanonin China Wengfu, da CSCEC na kasar Sin, da kamfanin Phosphate Misr na kasar Masar, sun sanya hannu kan yarjejeniyar gina wani katafaren kamfanin sarrafa sinadarin phosphoric da ake amfani da shi wajen hada takin zamani.

Kamfanonin 3 sun sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne a jiya Talata, matakin da ya share fagen ginawa, da kuma tafiyar da sabon kamfanin a Masar.

Cikin mahalarta bikin rattaba hannu kan takardun yarjejeniyar, hadda ministan albarkatun man fetur da sauran albarkatun kasa na Masar Tareq al-Molla, da jakadan Sin a kasar ta Masar Liao Liqiang, tare da kuma wasu jami'an kasar Sin.

Kamfanin wanda ake sa ran zai lakume kudi har dalar Amurka miliyan 848, za a gina shi ne a yankin Abu Tartour dake kudu maso yammacin kasar ta Masar. Bayan kammalar sa, zai rika samar da sinadarin phosphoric acid har tan miliyan 1 a duk shekara, domin sayarwa ga sassa masu bukata.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China