Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban manajan kamfanin dab'i na Yunguang na Zhejiang ya maida martani kan zargin da aka yiwa kamfaninsa na tilastawa fursunonin waje yin aiki
2019-12-24 19:33:33        cri

Kamfanin dab'i mai suna Yunguang na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin kamfani ne dake sayarwa kamfanin TESCO na kasar Birtaniya kayayyaki. A kwanakin baya ne, kafofin watsa labaran Birtaniya suka zargi kamfanin da tilastawa wasu fursunonin kasashen waje da ake tsare da su a wani gidan kurkuku mai suna Qingpu dake birnin Shanghai don su samar da katin bikin Kirismetti.

Game da wannan batu, gidan talabijin na CGTN na kasar Sin ya zanta da babban manajan kamfanin, Mista Lu Yunbiao, inda ya ce, zargin da aka yiwa kamfaninsa babu gaskiya a ciki ko kadan.

Rahotannin da wasu kafofin watsa labaran kasar Birtaniya suka ruwaito sun ce, kamfanin Yunguang ya yi amfani da wasu fursunonin kasashen wajen da ake tsare da su don su samar da katin bikin Kirismetti wadanda aka tura su kamfanin TESCO na Birtaniya, al'amarin da a cewar babban manajan kamfanin wato Lu Yunbiao, ba shi da tushe balle makama.

Mista Lu ya ce, yana matukar mamakin jin wannan labarin, saboda kamfaninsa bai taba yin irin wannan abu ba. Ya ce, ba shi da wata alaka da gidan kurkuku na Qingpu na birnin Shanghai, haka kuma ba su taba tuntubar juna ba. Wannan zargi karya ce tsagwaronta.

A cewar Mista Lu, dukkan kayan da kamfaninsa ya samar, ma'aikatan kasar Sin ne suka samar da su, kuma suna gudanar da ayyukansu daidai bisa dokar 'yan kwadago ta kasar.

Lu ya kara da cewa, dukkan katin bikin Kirismetti da kafofin watsa labaran Birtaniya suka ambata a zargin, an samar da su a kamfanin Yunguang, tun daga matakin farko har zuwa na karshe, wato tun daga aikin buga su har zuwa fitar da su zuwa kasashen ketare. Ya ce ya ji matukar takaici kan irin wannan zargin da aka yiwa kamfaninsa wanda ba shi da kangin gaskiya ko kadan.

Babban manaja Lu Yunbiao ya yi karin haske cewa, kaso 60 na kasuwancin kamfaninsa cinikin waje ne, kana kuma a kowace shekara, abokan cinikinsa na kasashen waje su kan gudanar da bincike da sa ido kan hakkin ma'aikata, da yanayi gami da matakan tsaro na kamfanin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China