Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tanzania ta sha alwashin karfafa dokokin kare gandun daji
2019-12-24 09:48:18        cri

Mataimakiyar shugaban kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, ta ce gwamnatin kasarta za ta ci gaba da karfafa matakan kare albarkatun gandun daji, da dazuzzuka, da yaki da farautar namun daji, domin kyautata rayuwar 'yan baya.

Samia ta bayyana hakan ne, ta cikin wani sakon talabijin da aka watsa, albarkacin ranar cika shekaru 60 da kafuwar yankunan kare albarkatun gandun daji na Serengeti, da Ngorongoro, tana mai cewa, kare albarkatun gandun daji, daya ne daga muhimman matakai na bunkasa harkokin yawon bude idon kasar wadda ke gabashin Afirka, harkar da a yanzu haka ke samun karin tagomashi.

Kaza lika a cewar ta, matakin kare albarkatun gandun daji, zai yi matukar taimakawa, wajen dakile mummunan tasirin sauyin yanayi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China