Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Gabon da ta ceto ma'aikatan jiragen ruwa guda hudu na kasar da aka yi garkuwa da su
2019-12-23 21:12:17        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Gabon ya bukaci bangaren Gabon da ya hanzarta yin bincike don ganin ya ceto ma'aikatan jiragen ruwa guda hudu 'yan kasar da aka yi garkuwa da su a tashar jiragen ruwan Gabon.

Kakakin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin, inda ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bin diddigin lamarin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China