2019-12-23 13:48:54 cri |
Jami'in mai kula da harkokin cikin gidan kasar, ministan harkokin labarai, kana kakakin gwamnatin kasar Gabon Edgard Anicet Mboumbou Miyakou, ya bayyana bayan taron gaggawa da aka yi cewa, sojojin kasar sun isa wurin nan take, a lokacin da suka samu labarin aukuwar lamarin, kuma bisa taimakon da 'yan sandan kasa da kasa suka samar musu, a halin yanzu, an kawar da kalubale a wannan yankin teku, kuma suna ci gaba da neman wadanda aka yi garkuwa da su. An kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta fara bincike kan wannan harka.
A halin yanzu kuma, 'yan jaridar kamfanin dillancin labarai na Xinhua, suna dukufa wajen tabbatar da asalin mutane 4 da aka yi garkuwa da su. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China