Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan hatsin da kasar Sin za ta samar zai kai sama da kilo biliyan 650 a shekarar 2020
2019-12-23 11:23:36        cri

Shugaban ofishin aikin gona na kwamitin tsakiya, kana ministan harkokin aikin gona da raya karkara na kasar Sin Han Changfu, ya bayyana a jiya Lahadi cewa, a shekarar 2020 mai zuwa, ya kamata a tabbatar da samun fadin gonaki na samar da hatsi mai muraba'in eka miliyan 95 a duk fadin kasar Sin, inda za a samar da hatsi sama da kilo biliyan 650 a shekarar 2020.

Mista Han ya bayyana haka ne yayin taron shugabannin ofishin aikin gona da raya karkara da aka yi a ranar 22 ga wata, ya ce, adadin hatsi da aka samar a shekarar 2019 ya kasance mafi yawa cikin tarihin Sin, har adadin ya kai biliyan 663.85, lamarin da ya sa, cikin shekaru 5 da suka gabata, adadin hatsi da kasar Sin ta samar ya wuce kilo biliyan 650 a kowace shekara, kuma, an girba cikin shekaru 16 a jere.

Ya kuma kara da cewa, ko da aka samu girba cikin shekaru da dama da suka gabata, amma a kan yi tangarda ta fuskar samar da hatsi. Har ma a wasu wuraren kasar, ana son raguwar samar da hatsi, lamarin da ya sa, ake fuskantar kalubalen samun raguwar adadin hatsi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China